====== Ali Nuhu Twitter Interview (#TareDaAliNuhu) - Saturday, September 12, 2015 ====== [[actor/ali_nuhu]] a Twitter: [[http://www.twitter.com/alinuhu|@AliNuhu]]\\ \\

Assalamu'alaikum. A Yanzu Haka kuma muna Tare da @alinuhu. #TareDaAliNuhu Kowa ya bude kunnen Shi.

— Hausa Proverbs (@Bahaushee) September 12, 2015

@alinuhu. ka jima kana yin harkar Fim, wane irin cigaba harkar Fim ta samu Daga lokacin zuwa Yanzu? @alinuhu #TareDaAliNuhu

— Hausa Proverbs (@Bahaushee) September 12, 2015

Ingantattun labarai, yanayin kayan aiki da makamantansu duk sun sauya. https://t.co/EVyaUfEcxA

— ali nuhu (@alinuhu) September 12, 2015

@alinuhu kana daya Daga cikin manyan Jarumai Na Kannywood, kuma ka samu lambobin girma da yawa, shin mi nene sirrin? #TareDaAliNuhu

— Hausa Proverbs (@Bahaushee) September 12, 2015

Juriya, jajircewa da mai da hankali kan aiki. https://t.co/DXHUpbMqyd

— ali nuhu (@alinuhu) September 12, 2015

Ranka ya dade, @alinuhu. Ko wane irin dabaru ne suke dauke da kai har tsawon wannan lokaci, ana ci gaba da damawa da kai? #TareDaAliNuhu

— IG: HausaTrends (@HausaTrends) September 12, 2015

Wannan kuma yin Allah ne saboda a Fagge irin wannan mutum bashi da dabara. https://t.co/f3uvFi5Haw

— ali nuhu (@alinuhu) September 12, 2015

@alinuhu. shin ko kaine jarumi Na Farko Daga Kannywood daya shiga Nollywood? Mi yaja hankalin Ali Nuhu? #TareDaAliNuhu

— Hausa Proverbs (@Bahaushee) September 12, 2015

Akwai irinsu Ibrahim Mandawari da Sani Muazu da Magaji Mijinyawa da Kasimu Yero duk sun rigani. https://t.co/L91T6oOSnC

— ali nuhu (@alinuhu) September 12, 2015

Tsakanin Nollywood da Kannywood, shin wa nene Ali Nuhu yafi Jin dadin fitowa a cikin fina-finan su? @alinuhu #TareDaAliNuhu

— Hausa Proverbs (@Bahaushee) September 12, 2015

Kannywood, don ba a raina mafari. https://t.co/eM9BcQVw4A

— ali nuhu (@alinuhu) September 12, 2015

@alinuhu kwanakin baya tunda Daga lokacin siyasa har bayan ta, wasu Na ganin kamar an samu rabuwar Kai tsakanin Yan Fim, Yaya abun yake?

— Hausa Proverbs (@Bahaushee) September 12, 2015

Babu rabuwar kai, muna nan tsintsiya madaurin ki daya. https://t.co/7Ho7bXYQnr

— ali nuhu (@alinuhu) September 12, 2015

@alinuhu Ko wanne yunkuri kuke yi a yanzu wajen ganin kun kubutar da kanku daga zarge-zargen cewa ba kwa raya al'adun Hausa? #TareDaAliNuhu

— IG: HausaTrends (@HausaTrends) September 12, 2015

@HausaTrends Amma a kullum nakan ce "Wanda ya raina tsayuwar wata ya has ya gyara" #TaredaAliNuhu

— ali nuhu (@alinuhu) September 12, 2015

Mutane suna yawan tsokaci Akan yadda ake sanya tufafi da kuma Yanayin fina-finan Nollywood, mi zaka ce Akan wannan? @alinuhu #TareDaAliNuhu

— Hausa Proverbs (@Bahaushee) September 12, 2015

Yawanci fina finan kudu fa labarin kudu suka kunsa saboda dole suturinsu su nuna haka. https://t.co/WjFhkDB5sh

— ali nuhu (@alinuhu) September 12, 2015

Wasu Yan Fim kamar Na Hollywood da Nollywood suna shiga siyasa bayan wani lokaci, ko Ali Nuhu nada ra'ayin shiga nan gaba? @alinuhu

— Hausa Proverbs (@Bahaushee) September 12, 2015

Gaskiya bani da ra'ayin siyasa https://t.co/kZcqXDto8i

— ali nuhu (@alinuhu) September 12, 2015

@alinuhu Ba ka ganin alaka da Gwamnati zata taimaki HausaFim, yadda ta taimaki Hollywood, Bollywood...? Me zai hana ku gyarota da gwamnati?

— IG: HausaTrends (@HausaTrends) September 12, 2015

Gwamnatin yanzu ba lallai sai yan fim sun shiga siyasa ba.Tana duba dacewa da cancanta ne a duk al'amuranta. https://t.co/Hik39qYkwG

— ali nuhu (@alinuhu) September 12, 2015

Daga Karshe, shin ta Yaya zaku daukaka martabar Hausa a idon duniya musamman ta fannin raya al'adu da kuma yada su? @alinuhu #TareDaAliNuhu

— Hausa Proverbs (@Bahaushee) September 12, 2015

Ta hanya samun hadin yan kallo, ma'ana su rika siyan fina finan da jigon su ya shafi al'adu. https://t.co/dKKXDCXf6t

— ali nuhu (@alinuhu) September 12, 2015

@alinuhu A karshe za mu so mu ji irin burin da kake da shi a nan gaba a harkarka ta HausaFim...? #TareDaAliNuhu

— IG: HausaTrends (@HausaTrends) September 12, 2015

Buri na ya kan zama sirri har sai ya tabbata mutane sa gani. https://t.co/fnK9vObTHO

— ali nuhu (@alinuhu) September 12, 2015

Mun gode daka kasance Tare damu, da fatan nan gaba mu samu wata dama mu tattauna sosai. Mun gode Bissalam. @alinuhu #TareDaAliNuhu

— Hausa Proverbs (@Bahaushee) September 12, 2015

Inn shaa Allah, nima na gode https://t.co/0ILDOxi7hd

— ali nuhu (@alinuhu) September 12, 2015

\\ \\ \\ \\ \\ \\ \\ [[actor/ali_nuhu]] a Twitter: [[http://www.twitter.com/alinuhu|@AliNuhu]]\\ \\ ===== Share this page =====