====== ’Yar fim Sadiya Gyale ta amerce ====== * Parent Category: Dandalin nishadi * Category: Dandalin nishadi * Published on Friday, 17 April 2015 00:00 * Written by Lubabatu I. Garba da Ibrahim M. Giginyu, a Kano * Hits: 9687 * http://aminiya.dailytrust.com.ng/index.php/dandalin-nishadi/9502-yar-fim-sadiya-gyale-ta-amerce A ranar Juma’ar da ta gabata ce fitacciyar jarumar fim din Hausa, Sadiya Muhammad wacce aka fi sani da [[actress/Sadiya Gyale]] ta amerce wanda ya kawo karshen barinta masana’antar fim din dungurungum. Auren da jarumar ta yi shi ya kawo karshen rade-radin da ake yi cewa akwai alakar soyayay tsakaninta da jarumi [[actor/abubakar_baballe_hayatu]], duk da yake jaruman sun sha musanta batun soyayay a tsakaninsu inda suke cewa akwai kyakkyar fahimta da abokantaka a tsakaninsu. An dauki tsawon shekaru rabon da a ga fuskar jarumar a cikin fina-finan Hausa, inda masu kula da al’amuran yau da kullum ke ganin cewa hakan ya faru ne sakamakon yin aure da aminiyarta kuma abokiyar sana’arta, Zainab Raga ta yi. Hakan ya sa jarumar ta dakatar da yin fim don ta mayar da hankalinta wajen sama wa kanta mijin aure. Aminiya ta rawaito cewa an daura auren jarumar tare da angonta Abubakar Muhammad ne a safiyar ranar Juma’a, a unguwarsu da ke Wudilawa. Angonta ya biya Naira dubu 50 a matsayin sadaki. Ana ganin cewa aurenta yana daya daga cikin aure-auren da kusan dukkanin masu ruwa da tsakai a sana’ar fim suka halarta. Daga cikin wadanda suka halarta akwai [[actor/Shehu Hassan Kano]] da Kabiru Miakaba da [[actor/Ali Nuhu]] da Bala Anas Babinlata da sauransu. Daga cikin fina-finan da ta yi sun hada da [[film/Gyale]] da [[film/Gidan Gado]] da [[film/Jaraba]] da [[film/Gudun Kaddara]] da Gwamnati da Gwanaye da Jamhuriyya da [[film/Kishiya ko ’Yar uwa?]] da [[film/Tutar So]] da [[film/Ummi]] da [[film/Gidan Iko]] da [[film/Gara]] da sauransu.