====== Fauziya D. Sulaiman ====== {{ cast_and_crew:writer_fauziya_d_sulaiman.png?228 }} \\ **Occupation** [[:cast_and_crew?dataflt=occupation%3DWriter|Writer]] \\ **Hometown** Fagge, Kano, Nigeria Fauziyya D. Sulaiman wadda aka fi sani da Matar Bello Q far Q an haife ta a unguwar Fagge a Shekarar 1981 ta yi karatuna na Firamare a Makarantar Festival Primary School, daga nan wuce makarantar ‘yammata ta kwana Government Girls Secondary School ‘Yar gaya a shekara ta 1993, bayan ta kammala karatunta na Jiniya ta koma Makarantar Government Girls College Dala ta karasa karatunta daga 1995 zuwa 1998. Daga nan ta yi aure a shekara ta 1999. A shekara ta 2003 ta koma karatu a Makarantar College of Health Sciences, School of Hygiene in da ta yi Diploma a kan Assistant Nutritionist. Daga nan ta yi Certificate a Makarantar School of Management, akan Hotel and Catering Services. \\ \\ \\ \\ A game da rubutu kuwa ta fara rubuta littafi a shekarar 2002, in da littafi na farko mai suna Me na yi mata?. Daga nan ta ci gaba da rubuta littafi da suka hada da: - [[film/Kishin Banza]] - [[film/Guduna Ake yi]] - [[film/Rayuwar ‘Ya Mace]] - [[film/Mece ce Rayuwa]] - [[film/Burin Raina]] - [[film/Karshen Wahala]] - [[film/Labarin Zuciya]] - [[film/Matsalar Mace]] - [[film/Mijin Uwa]] - [[film/Auren Kudi]] - [[film/Duk Abinda Namiji Ya yi]] Fauziyya mamba ce a Kungiyar Marubuta ta Najeriya reshen jihar Kano kuma tana rike da mukamin jami’a a majalisar gudanarwa ta Kungiyar tun watan Maris na 2009 har zuwa 2010. Daga nan aka sake zabenta a dai wannan mukami daga watan Maris na 2010 har zuwa watan Maris na 2012 insha Allahu. Daga/by Professor Yusuf M. Adamu at Wednesday, March 31, 2010 http://marubutanhausa.blogspot.com/2010/03/fauziyya-d-sulaiman.html ===== Hira da AREWA24 ===== \\ Published by [[producer/arewa24]]'s [[film/kundin kannywood]] on Dec 5, 2014\\ ===== Share this page =====