User Tools

Site Tools


actress:hadiza_gabon.

Hadiza Gabon

hadiza_gabon.jpg
Occupation Actress
Born Hadiza Aliyu on June 1, 1989 (Age: 34 years old) in Gabon
Years Active 2007-Present
Social media Instagram, Twitter, Facebook

Hadiza Gabon began her acting career in 2009 and since then, she has not stopped. As one of the many talented actresses in Kannywood, her acting skill has shown that she’s one of those to be reckoned with in the industry. She has featured in many Hausa movies like “Ali yaga Ali”, “Haske”, to mention a few. Her fan base of 433, 000 on her verified instagram account, shows that Gabon is on her way to the top.1)

Hadiza Gabon Images

Biography

Hadiza Gabon also known as Hadiza Aliyu is a Hausa actress born and brought up in Gabon. She's generally considered by many in the industry to be a good role model as she appears to be highly cultured and well dressed. Her mother is Fulani from Mubi, Adamawa state. She did her Primary school in Gabon, got a diploma in French. She also learned to speak Hausa and her native language Fulu. She first arrived in Nigeria in 2007.

Career

Upon developing interest to join Kannywood, she decided to settle in Kaduna with her cousin. She then met with Ali Nuhu and sought for his assistance in launching her acting career. She considers him to be like her brother, mentor, and adviser. Aminu Shariff (Momoh) is another of her mentors. She entered into Kannywood - the Hausa film industry in 2009 where she started acting in the film Artabu (A Mazauna) (2009).

History and interview with LEADERSHIP Hausa

Tarihin Hadiza Aliyu, wacce aka fi sani da Hadiza Gabon, ‘yar asalin kasar Gabon ce. An haife ta ranar 1 ga Yuni, 1989 a Libreville, babban birnin kasar ta Gabon. A nan ta fara karatunta tun daga firamare har har ya zuwa babbar makarantar gaba da sakandare, inda ta karanci difiloma a fannin yaren Faransa a kwalejin Ecol de Francaise Garbonnaise a shekarar 2006.

Ta shiga harkar finafinan Hausa ne a shekarar 2008, lokacin da ta dawo nan Nijeriya, sannan tana daya cikin jaruman da suka shiga masana’antar fim da kafar dama, domin a cikin dan kankanin lokacin da ta fara fim, kusan sai da ta fara tafiya kafada da kafada da manyan jaruman da ake ji da su a cikin harkar fim din. A lokacin ganawarta da Editan wannan jaridar, AL-AMIN CIROMA, jarumar ta bayyana wa masu karatu irin sauyin rayuwa da samu kanta a ciki gami da yadda ta ke kallon sana’ar fim.

Idan kun shirya, ga takaitacciyar hirar Gabon da jaridar LEADERSHIP HAUSA:

Yaushe kika shiga masana’antar fim, kuma mene ne dalilin kiranki da Hadiza Gabon?

Dalilin kirana da wannan sunan saboda ni ‘yar asalin kasar Gabon ce. A can aka haife ni, na yi karatuttukana, har ya zuwa difiloma. Sannan a lokacin da na dawo Nijeriya, inda nake zama da wata ‘yar’uwata sai wannan aka lakaba min wannan sunan, wanda a yanzu idan ba Hadiza Gabon ka kira ba, da wuya a yi saurin shaida ni. Na fara sha’awar fim ne tun ina Gabon, saboda a can ma mu na kallon finafinan Hausa, akwai finafinan da su ka birge ni tun ina makaranta, sai na ji a raina, ina ma da a ce ni ma wata rana in zama jarumar fim. A haka dai na rika wannan sake-saken, har Allah ya karbi addu’ata a cikin shekarar 2008. Fim din da na fara yi shi ne Artabu, wanda Darakta Ishaq Sidi Ishaq ya shirya a Jos.

Kasancewarki ‘yar asalin Gabon, wanda daga dukkan alamu, ke ba Bahaushiy a ba ce, wadanne irin kalubale kika fuskanta a lokacin da ki ka shiga finafinan Hausa, wadanda dari-bisa-dari da fitacciyar Hausa ake shirya su?

(Dariya), gaskiya kam, na samu matsaloli da dama, musamman wajen karya harshena domin yin magana da karbabbiyar Hausar adabi. Ni dai Bafulatana ce, kuma ina jin yaruka kusan guda uku, banda Hausa. Na iya yaren Faransanci, Puno da kuma Fulfulde. Amma a lokacin da na zo nan, duk da ina iya magana da Hausar, duk da haka, sai na jajirce wajen karyar da harshena, har kuma Allah Ya ba ni sa’a ina dan tabukawa.

Wadannan yaruka da ki ka kira, dukkansu a can kasar taku kika koyo?

Ka ga a Gabon, yaren Puno shi ne kusan babban harshen da ake tinkaho da shi, sai kuma Faransanci da Fulfulde. Fulanin dai ba su da rinjaye a kasar, ‘yan tsirarru ne. Masu rinjaye su ne Puno. Saboda haka, ka ga ya zama dole mutum ya iya yarukan gaba daya.

Wanne irin sauyin rayuwa ki ka samu sa’adda da ki ka shiga fim?

Ba wani gaggarumin sauyi da na samu, illa dai fim wata masana’anta mai alfahari da kirkira da jajircewa wajen nuna kwazo da bajinta a cikin duk ayyukan da mutum ke yi. Idan ka kasance a cikin harkar, ya zama dole ka rika kallon kanka a matsayin jarumi, mai kokarin samar da sabbin abubuwa. Muddin dai ka na son a rika damawa da kai, to fa ya zama wajibi har kullum ka luzumci nemar wa kanka mafita. A nan, ina nufin a duk lokacin da aka ba ka jarumi ‘Script’ na fim, abu na farko da zai lura shi ne, ya tabbatar ya isar da sakon da aka rubuta masa a labarin, ta yadda daraktan zai yi alfahari da kai. Sannan masana’anta ce mai cike da rige-rige. Kowa na son ya yi abu mai kyau, ba wanda ke bukatar bata lokacinsa a banza. Saboda haka, sauyin rayuwar da mutum zai samu shi ne, har kullum kana fafarniyar tsayuwa da kafarka ne. Ba sana’a ba ce ta ragwaye ko marasa basira. Kuma wannan bai takaita ga jarumai kadai ba. Duk wanda ka gani a ciki, kokarinsa shi ne; ta yaya zai fi kowa iya yin abu da kyau. Misali, mai kwalliya, a kowanne lokaci, ya na kokarin nunawa furodusa ko darakta ya san aikinsa kuma kwararre ne a fanninsa, haka mai haska fitila, mai kula da sauti da kuma masu daukar hoton bidiyo. Kai, hatta masu girki da masu bayar da hayar kawan da ake sawa da motoci, kowa dai kokarin nuna bajintarsa yake. Don haka, masana’anta ce mai tarin fitattun mutane ko kuma mu ce hazikai a kowanne fanni. A matsayina na jaruma, a kullum ina kara godiya ga Allah, ina kuma fadada tunanina ta yadda zan rika isar da sakon da darakta ya ba ni, daidai wa daida. Abin da na fara fahimta a harkar fim shi ne, ba wai zama fitacce shi ne mai wahala ba, amma yadda jarumi zai rike kambunsa har ya zuwa wani lokaci shi ne babban kalubalen. Abin da nake nufi shi ne, sai ka ga wani da ya shiga fim sau daya, shi ke nan, sai tauraruwarsa ta fi ta kowa haske a lokacin, amma daga bisani, sai ka neme shi ka rasa.

Mene ne dalilin hakan?

Ka ga kenan dole ka tsaya kyam domin kare martabar kambin da Allah Ya ba ka. Duk da ba mai zamaninsa, ya ci na wani, amma dai babban kalubalen da jarumai ke fuskanta da kuma saurin rayuwa a cikin masana’antyar fim su ne yadda zai kare martabar kambunsa a lokacin gasa.

Yaya ki ke kallon masana’antar fim din a yanzu?

Harkar fim ya na bunkasa fiye da lokutan baya. A yanzu kam ko makaho ne ya ji irin yadda ake tace sauti, ya san lallai an ci gaba. Sannan idan ka kalli finafinan, za ka tabbatar su na da inganci fiye da da can baya. Ina ganin ta kowacce mahanga, fim ta samar wa kanta mazauni a cikin al’umma. Babban abin da ke birge ni shi ne irin yadda masana’antar ke samar da kwararrun ma’aikata da kayayyakin aiki na zamani.

A da, sai ka ji a maganar ‘Nigerian films,’ ana cewa sun zarce finafinan Hausa da komai. To yanzu fa?

Duk da tsarinsu daban da namu, amma mutum zai fi jin dadin kallon finafinan Hausa na wannan zamani a kan na Turanci. Dalilai da dama sun nuna hakan. Ka ga na farko, a duk lokacin da kake kallon finafinan Turanci na Kudu, idan kana cikin iyalinka da yara, sai ka ji a ranka ba cikin natsuwa, saboda a kowanne lokaci, za ka iya ganin namiji ya rungume mace, ya sumbace ta, ko kuma mace ta fito rabi tsirara, ta hau gado da namiji da dai abubuwa masu dama, wadanda da gani, ka san iskanci ake yi. Hatta kananan yara na fahimtar hakan. Don haka, muddin magidanci ya san ciwon kansa, wallahi da wuya ya samu natsuwa wajen kallon finafinan Turanci na Kudanci a cikin iyalinsa ko tare da wadanda yake jin kunyarsu. Sai dai ya kalla shi kadai ko cikin abokai.

To amma finafinan Hausa fa?

Ba za ka taba ganin namiji ya rike hannun mace ko a nuna mace tsirara kan gado da wani kato ba. Wannan ba karamin nasara ba ne masana’antar fim ta haifar. Finafinan Hausa, duk da ba ka rasa samun akasi nan da can ba, amma su na kokarin wakiltar al’ummar da ta san inda rayuwa ta dosa. Saboda haka, ni dai ina kallon masana’antar nan a yanzu tana ci gaba kwarai kuma idan aka mara mata baya, za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da al’umma gaba.

Za mu iya kiranki da ‘SuperStar,’ ma’ana fitacciyar jarumar finafinan Hausa?

(Dariya)… ai kowa ma fitacce ne ai. Duk wanda zai fito a fim a matsayin jarumi, sai ka same shi mutum ne da ke da dimbin baiwa. Ni ina ganin ko sau daya mutum ya fito a fim zai iya kaiwa kololuwa. Amma idan aka yi maganar fitattu, ko kuma yadda ka ce SUPERSTAR, a ganina ba mutum ke sanya wa kansa sunan ba, illa masu kallo da alkalai. Kawai dai, mun shigo, kuma mu na iya kokarin ganin an dama da mu. (Dariya).

Gaya mana irin badalar da ki ka sani a harkar fim?

(Tunani) A duk lokacin da aka ambaci fim, wanda bai fahimci me ake magana a kai ba, sai ya dauka duk wanda ke ciki, ya kware a harkar iskanci. Wannan ko kadan ba haka yake ba. Abin kawai da zan ce a nan shi ne, mutumin kirki, tun asalinsa na kirkin ne, haka kuma mutumin banza, tun tasowarsa haka yake. Kuma zaka iya samun haka a kowane fanni na rayuwa. Ba abin da ba ma ji da gani a yau.

Masu aikata masha’a ko iskanci a kullu yaumin din nan, duk ‘yan fim ne?

A’a…! Ba inda ba za ka samu mai kyau da baragurbi ba. Da wannan sana’a ta fim, za ka samu wani a ita ya dogara wajen samun na sawa a bakin salati. ‘Yan kasuwa da dama sun yi dimbin arziki da fim. Masu buga fosta, masu sayar da CD, masu safarar kayan daga gari ya zuwa gari, masu daukar hoton bidiyo da na kati, teloli, masu na’urar buga takardu da kuma uwa uba jaruman da ke fitowa a shirin. Ka ga kenan idan ka yi jam’in cewa harkar badala ne kawai ake yi a ciki, ka dauki alhakin mutane da dama.

Wanne fim ya fi haska ki, har tauraruwarki ta yi fice?

Ina son duk finafinan da na yi, amma wanda ya fi haska ni shi ne ‘Babban Zaure.’

Kina da saurayi a cikin fim?

(Dariya) Ban taba yin saurayi cikin ‘yan fim ba. Ai soyayyar ‘yan fim ba ya boyuwa. Idan mutum yana yi kowa zai sani ai.

Kina nufin ba wanda ya taba tayawa?

(Dariya) Dan jarida, na ce maka: Babu!

(dariya) Za ki iya auren dan fim?

Aure ya kan zo ne kamar ajali. Idan har Allah Ya nufa mijina na cikin wannan masana’atar sai na roki Allah, ya zama shi ne mafi alheri a rayuwata. Ba komai zan iya auren dan fim. Yawanci masoyanku na kukan cewa kuna wulakanta su, musamman idan su ka kira ku a waya.

Yaya huldarki da masoyanki?

Gaskiyar magana ina amsa waya sosai, duk wanda ya kirani, musamman idan ba a lokeshin nake ba, zan amsa. Kuma ina fatan wadanda za su kira, su ji mutum bai amsa ba, za su gane, saboda duk lokacin da mutum yake lokeshin, ana kuma daukar shirin fim, ba zai iya amsa waya ba.

Yawanci mene ne masoyanki su ke fada miki a waya?

Da yawa daga cikin su addu’a suke min da sakonnin fatan alheri. Kuma su kan ba ni shawarar cewa duk abin da zan yi, na tabbatar cewa aure shi ne ya kamata na sanya a gaba da sauransu.

Wane ne gwaninki a fim?

Mutum daya ke birge ni a yanayin aktin. Wannan kuwa ba kowa ba ne, illa Aminu Ahlan Shariff (Momoh).

Mene ne sakonki ga jama’a?

Na gode da addu’o’i da fatan alheri kuma su ci gaba da yi mana addu’a. Mun gode, mun gode

Filmography

Films

VOA Hausa Yau da Gobe Interview Mar 20 2015

A Tribute video/song to Hadiza Aliyu Gabon

Share this page

actress/hadiza_gabon.txt · Last modified: 2022/05/27 04:05 by admin