User Tools

Site Tools


actor:rabilu_musa_dan_ibro.

Dan Ibro

dan_ibro.jpg
Occupation Actor, Comedian
Born Rabilu Musa Dan Lasan aka Dan Ibro from Wudil, Kano, Nigeria on December 12, 1971
Died on Tuesday, December 9, 2014 (age 44) in Kano, Nigeria1)2)3)4)5)6)

Personal Life

An haifi marigayi Rabilu Musa Ibro a shekarar 19717). Ya yi karatun Firamare dinsa a Danlasan da ke cikin karamar hukumar Warawa. Sannan kuma ya yi Sakandare a Kwalejin horon malamai ta Wudil (Teachers College). Daga nan ne ya shiga aikin gidan Yari (Prison Service) a shekarar 1991. Ya yi shekara takwas Ya na aikin Gandiroba inda ya kai matakin insfekto, daga nan ne ya bari ya cigaba da sana’ar wasan kwaikwayo.

Rabilu Musa Ibro ya fara sana’ar Fim a tun ya na aji uku na makarantar sakandare. Ya na da Mata da Yara hudu ko uku akwai : Jamila, Kubra, Auta.

Daga cikin yaransa akwai: Akwai Faisal, Jawahid, Lawiza, Abdul-Mummuni, Sannan akwai Asma’u, Annabe, Sa’adiyya, Akwai wani yaro kuma da ya Haifa ya sa sunan mai gidansa wato Baba Yaro.

Kafin Rasuwarsa Ya bayyana Ciroki a matsayin dan wasan hausa abokin sana’ar sa da ya fi burgeshi.

Da aka tambayi Rabilu Musa ibro dan wasan santimental da ya fi burgeshi sai yace “ Adamu Usher, ka ga wannan, yana bani sha’awa. Saboda ba shi da girman kai, ba zan manta ba lokacin rasuwar kulu da Yautai, tun daga farkon rasuwar mu na tare da su.” In ji Ibro

Daga cikin dubunnan fina finansa ibro ya bayyana cewa ya fi son wadannan fina finai “Akwai Kauran Mata, Kowa Ya Debo Da Zafi, da kuma Mai Dawa.

Ibro ya bayyana ya fi son tuwon dawa a bangaren abincinsa, fannin sutura kuma sai yace “Na fi son yadi wanda zan shekara da shi ina gurzawa, ba in sa Shadda ba kwana biyu in ga tana kodewa.

Da aka tambayi Marigayi Ibro a lokacin ya na raye me ya fi bakanta masa rai a kan harkar sana’arsa sai yace“ Ni abinda yake bata mani rai kawai a wannan sana’a bai wuce rashin hadin kan ‘yan wasa ba.

Rabilu Musa Ibro Ya amsa kiran mahallicinsa ya na da shekaru 43, a duniya. Allah ya kyautata makwanci.

An dauko daga mujallar GIDAUNIYA via FIMHAUSA/HausaFIM (Twitter: @Fimhausa, Instagram : fimhausa, Facebook: http://facebook.com/hausafim)

Videos

Binciko bidiyon Ibro a YouTube

ZAKI A WAJE KIYASHI A GIDAALLAH YA JIKAN IBRO

Posted by Waziri Aku on Thursday, August 27, 2015

Death

  • Died at the age 44, leaving behind three wives and 15 children.8)
  • Ga saututtuka game da mutuwarsa (Audio clips regarding his death):Filmography

Films

Share this page

actor/rabilu_musa_dan_ibro.txt · Last modified: 2017/11/12 19:50 by admin