User Tools

Site Tools


film:sarki_jatau.

Sarki Jatau

SARKI JATAU

“Sarki gwangwala, a hau ka a zame, ka hau mutum ka zauna daidai”.

Daga taskar koje Sarkin labari, malami uban malammai Dr. Alhaji Abubakar Imam, OBE, CON, Allah ya jikansa da rahama. Kana, daga shahararren kundin littafinsa wato Magana Jari Ce; - Yaro bada kudi a gaya maka! Kana, bisa ga amincewar ma’adanar taskarsa.

Wasu aminan tagwayen kanfunan shirya finafinai da ke Abuja wato Grafarts pictures da Hashwannar Movies ke gabatar muku da fin din SARKI JATAU wanda Bashir Abdullahi Rijau ya shirya, ya kuma ba da Umarni.

A tsanake, kuma cikin hikima da raha an kawo labarin mulkin wani mutakabbarin Sarki da kuma irin jajircewar talakawansa. Bayan an sha dan karen dariya, kazalika masu mulki za su fahinci cewa banbancinsu da talakawansu ba ta wuce ta tsoron Allah ba, ko watakila irin tarin rigunan da suke ado da su. Da kuma zarar ba rigar sai ga Sarki ya zama mahaukaci.

Umm uh hmm, Dare daya Allah kan yi Bature in ji masu iya magana. Labarin da ku ka dade ku na karantawa a takarda, yau ga shi za ku kalleshi a matsayin fim. Kada ku yarda a ba ku labari.

ZAI FITO NAN BA DA JIMAWA BA!

Daga: Bashir A. Rijau

(source)

Sarki Jatau Trailer

Share this page

film/sarki_jatau.txt · Last modified: 2015/07/22 03:14 (external edit)