User Tools

Site Tools


film:sarki_jatau:hausa_leadership_article.

Bidiyo Sarki Jatau Sabon Salo Ne A Harkar Kannywood

http://hausa.leadership.ng/?q=node%2F466
Bidiyo Sarki Jatau Sabon Salo Ne A Harkar Kannywood —Bashir Rijau

Haifaffen Neja, Alhaji Bashir Abdullahi Rijau fitaccen qauyen Rijau a Jihar mashiryin fim ne na Hausa, wanda ya fara da hannun dama. Jim kadan bayan kammala karatunsa a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, Rijau, wanda yake kwararren mai sarrafa zane-zane ta fuskar na’ura mai kwakwalwa, ya yi ayyuka daban-daban, wadanda suka shafi kimiyyar da ya karanto a jami’a. Bashir ya fara aiki ne a kamfanin dab’i na Heritage Press Abuja, inda daga bisani ya kafa nasa kamfanin, mai suna Grafarts Pictures.

A cikin wannan tattaunawar da ya yi da wakilinmu, AL-AMIN CIROMA, Rijau, ya bayyana yadda sha’awa ta sanya ya fada tsundum cikin farfajiyar shirin finafinan Hausa. Inda ya fara da shirya wani kasaitaccen fim din da ya ja hankula a wancan lokacin, wato WASAN MAZA. Daga nan kuma ya kara shirya wani fim mai suna MASHA ALLAH.

Fasihin bai tsaya nan ba, domin kuwa ya kasance daya daga cikin masu taka muhimmiyar rawar ganin an kawo ci gaba a harkar Kannywood. A bisa wannan dalilin ne Bashir tare da wadansu abokan sana’arsa, suka kirkiro wata mujalla, mai suna, ABIDA, wadda ba a taba samun irin ta a duniyar finafinan Hausa ba, musamman kyan tsari, hotuna da zubin labaran mujallar. Bayyanar Abida ya haifar da ci gaba ta fannin duniyar dab’i, musamman na mujallu, inda yawancin suka fara kwaikwayar irin tsarin da mujallar ta Abida ta zo da shi.

Dadin dadawa, kwanan nan kuma, Hazikin ya kara shiga lokeshin, inda ya shirya wani kasaitaccen fim din da ake tunanin ba a taba shirya irin sa a tarihin masana’antar fim na Hausa ba. Fim din mai suna SARKI JATAU, shi ne irin sa na farko, musamman da aka yi amfani da gundarin labarin fitaccen marubuci, Marigayi Dakta Abubakar Imam. Mashiryin shirin, wanda shi ne Furodusa kuma darakta, har ila yau, ya dan gutsuro mana kadan daga cikin abubuwan da suka shafi fim din da sana’ar fim baki daya. Bismillanku:

Mun samu labarin ka fara aikin wani sabon shirin fim na musamman. Ko za ka warware mana zare da abawa kan wannan fim?

To, alhamdulillahi, wani abu da ban fadi ba a cikin tarihi na shi ne ni mutum ne mai sha’awar adabi na Hausa, duk da yake na karanta Hausa a matakin sakandare, inda na samu babban maki wato ‘A1’. Haka kuma mukan karanta litattafan Hausa, irinsu ‘Ruwan Bagaja,’ ‘Magana Jari Ce,’ da sauransu a cikin aji. Ko da yaushe na kan zama mai sha’awar ganin na samu dama na yi amfani da daya daga cikin litattafan da Dakta Abubakar Imam ya wallafa.

A lokacin da na kuduri aniyar shirya wannan sabon fim din nawa, wato SARKI JATAU, sai na rika jin tsoron ko idan na je na nemi iznin yin amfani da daya daga cikin labaran zan iya samun matsala…? da sauransu. A haka na rika sake-sake a zuciyata, amma da na yanke hukuncin neman izini daga mawallafan littafin, sai na aika da takardar neman izini a rubuce, don yin amfani da wani labari, wanda ya ba ni sha’awa mai suna, ‘Labarin Sarki Jatau,’ cikin yardar Allah sai ga shi sun ba ni iznin ci gaba da aiki.

To a nan ne muka fara aikin fim din SARKI JATAU, wanda a sannin mutane ne cewa idan za a yi fim irin wannan akwai kare-kare da rage-rage, haka nan mu zauna muka yi ‘Screen Play,’ da sauransu. Sannan kamfanoni biyu ne, GrafArts Pictures da Hashwannar Mobies Abuja suka dauki nauyin fim din.

Idan na fahimce ka, kana nufin kun dauko labarin fim din daga littafin Dakta Abubakar Imam kenan? Wanne littafi ne daga cikin litattafan nasa?

Daga cikin ‘Magana Jari Ce’ na Uku muka dauko labarin, wanda ya wallafa a shekarar 1937-39, sunan labarin, kamar yadda na fada a sama, ‘Labarin Sarki Jatau.’

A yayin da takwarorinka, wato furudososi suka himmatu kan shirya finafinan kan wasu bangarori na rayuwa, irin soyayya, harkar iyali da zamantakewa, sai ga shi kai kuma ka zabi labarai irin na da. Mene ne hikimar yin hakan?

Wato abu na farko da na lura da shi shi ne mu a nan Arewa, ba mu da kauron labarai, ba mu da yunwan labarai sahihai, wanda yake ya kamata mu ba ‘ya ‘yanmu da na baya su ma su amfana. Manyan marubuta da suka gabata, sun yi rubuce-rubuce da dama, wadanda ya ke abin bakin ciki shi ne a yanzu an mayar da su a wurin adana, ba don a karanta su a fahimta ba. Ni kuma a nawa tunanin idan dai labari mutum ya ke so, ya zo Arewacin Nijeriya, to akwai duk wani labari da ya ke bukata. Sai na tambayi kaina, me zai hana tun da mun tarar da litattafan da suka rubuta, me zai hana mu mayar da su cikin fasahan zamani don ‘yan zamani su amfana? Domin idan ka ce wani ya yi karatun Hausa ma sai ka ga abin ya gagare shi, amma idan ya gani a fim, sai ka ga ya zauna ya kalla kamar yadda zai iya zama ya kalli labarai da sauransu. Wannan shi ne dalilin yin haka.

Ko za ka bayyana mana yadda yanayin daukar fim din ya kasance, kama daga zaben ‘yan wasa, kudaden da a ka kashe, da kuma kayayyakin da aka yi amfani da su…?

Gaskiya, mun yi amfani da kamarori masu inganci, wadanda a yau duniyar fim ke alfahari da su, misali mun yi amfani da kamara, kirar Canon 7D, to ba zan ce mune na farko da muka fara aiki da ita ba, amma dai muna da tabbacin cewa ainihin masana aiki da kamarar mun samu hadin kansu mun yi aiki tare. Kuma da yake tarihi ne, mun je gidan adana al’adun tarihi na Kano, sun ba mu aron wasu, sun kuma yi mana kyautan wasu a matsayin gudummawa. Mun yi amfani da dawakai, har fadar Sarkin Kano an taimaka mana da masu nadin rawunna. ‘Yan wasa kuwa, mun zauna, mun duba labarin, sai muka dauki wadanda su ka dace.

Akwai wadanda suka dage da shirya irin wadannan finafinan, amma daga baya, idan sun fito, sai ka ga sam ba su kai yadda ake so ba. Kuma za ta tarar jama’a suna ta korafi dangane da su, me ka ke ganin zai bambanta wannan aikin na ka da sauran finafinan?

Bari na fada maka wani abu. Kuma ya zama dole ya kuranta kamfanina. Alal misali, fim dina na farko, wato ‘Wasan Maza,’ zan iya tinkahon cewa shi ne fim din Hausa na farko da a ka fara bugawa a faifen CD na 5mm a 10mm, wanda kafin fitowarsa babu irin wannan. Don haka, komai yana bukatar mutanen da za su jajirce.

Gaskiya mataki na farko da zai bambanta fim din nan da saura shi ne ba za mu sake shi a CD irin wanda mutane su ka sani ba. Za mu yi shi ne a tsarin DBD. Saboda ba ma bukatar kyan hoto da sauti ya ragu ko kadan. Saninmu ne cewa hoto da sauti su ne kyan fim. Saboda haka, za mu tabbatar wa dan kallo, zai ga sabon abu a fin din SARKI JATAU.

Ka tabo batun DBD, sai ka tuna min da yadda furodusoshi ke kuka game da illar da barayin zaune ke yi musu. Alhaji Bashir, wacce hanya za ku bi ku magance wannan matsalar, wadda ke neman karya masana’antar?

Lallai ka sosa min inda ke min kaikayi, satar fasaha yana daya daga cikin manyan kalubalen da ke fuskantar finafinan Hausa. Yanzu ma an fito da wani tsarin satar fasaha ta hanyar MP4. Inda za ka tarar mutum yana zaune, sai a tura masa fim kacokan ta hanyar na’urar BLUETOOTH. To duk wannan mun zauna mun yi shawara a kai. Sai dai akwai kuma albishir da za mu yi wa kawunanmu, gwamnati ta fito da sabbin hanyoyi na fatattakar barayin boye, sun dan yawaita kame, dauri da kuma horo mai tsanani. Yanzu ka ga an fito da hanyar tsarkake gidajen kallo, wato tsarin BOD OFFICE. Ka ga alal-misali, a Kano kawai, an kiyasta akwai gidajen kallo sama da dubu goma. To, idan har masu gidajen kallo, za su zo kai-tsaye su sayi finafinai a hannun furodusa ko da dubu daya ne, sannan su je su nuna a gidajen kallon na su, ka ga kenan furodusa, zai iya samun naira milyan goma. Maimakon yadda suke shiga kasuwa su sayi finafinan naira dari biyu su ke su nuna. Idan har aka bi wannan tsarin, kafin ma fim din ka ya shiga kasuwa, ka fitar da kudinka, sannan duk abin da ka samu a kasuwa riba ce. Wadannan kadan ne daga cikin hanyoyin da muke tinkaho da su, shi ya sa mu ka shigo harkar gadan-gadan.

Darakta Bashir, wanne albishir za ka yi wa ‘yan kallo game da SARKI JATAU. Mene ne ka ke ganin zai bambanta fim din ka da na saura?

Albishir na farko shi ne su saita komi bisa tsarin kwarewa. Tabbas ‘yan kallo za su gamsu da tsarin hoto. Za su hoto rangadau, saboda kamarorin da muka yi aiki da su. Tsarin da muka bi wajen daukar sauti ma daban ne da yadda ake daukar sauran finafinai. Alal-misali, ‘audio,’ wato sautin dukkanin jaruman, mun dauka ne a wata kamara ta musamman, haka ma bidiyo, wato hoto, mun dauke su ne da kamara ta musamman, to daga baya ne a wajen tacewa, wato ‘editing,’ za mu saisaita hoton da sauti su tafi bai daya. Ka ga kenan, za ka tabbatar akwai sauti gami da hoto ingantacce.

Gaya mana fitattun jaruman da suka taka rawa a cikin wannan fim din. Sannan wane ne ya fi burge ka a cikinsu?

Cikin jaruman da suka fito dai akwai wani bawan Allah dan Jos, mai suna Tijjani Faraga, akwai Rabi’u Rikadawa, wato DILA, akwai Mustapha Musty, Sadi Sawaba, Hadiza Mohammad, akwai Bashir Nayaya (Dan Magori). Haka kuma Shugaban Arewa Filmmaker na Kasa, Baba Karami shi ma yana ciki. Ba zan manta da rawar da Tijjani Asase, Nabila, da Aisha Dankano suka taka ba. Haka kuma mun gayyato Jaruma, Hauwa Katanga, wadda aka daina jin duriyarta, a fim dinmu ta kara dawowa ruwa.

Batun kuma wanda ya fi birge ni… a matsayina na daraktan fim din kowa na jinjina masa. Kai, hatta wadanda suka fito irin kananan rols, sun birge ni. Amma duk inda aka taru, sai an samu fitacce. Gaskiya na jinjina wa wanda ya fito a matsayin SARKI JATAU, wato Faraga. Lallai ya taka muhimmiyar rawa. Ni ma a matsayina na darakta, sai da na cira masa hula, saboda akwai inda muka je shutin a cikin kogi, a karkashin gadar Tamburawa, wanda yake baicin sanyin safiya, an umarce ni da ya shiga cikin kogin ba tare da kayan jikinsa ba. Na jinjina masa kwarai saboda ya bayar da abin ake so. Sannan so da yawa kuma, ya kan fito babu kaya a jikinsa, kamar yadda ya bayar, duk da yake mu mun san ba tsiraran yake, amma wannan wani ‘rol’ da yake da ‘challenges,’ wato kalubale da yawa, amma ya jajirce, yana yi komai daidai wa daida. Hakika ya taka rawar gani.

Kuma abin da ya fi ba ni sha’awa da ‘yan wasana duka shi ne, ko da yake, saboda mun ba su ‘script,’ kusan wata guda kafin a fara shutin, saboda mun jaddada musu tsohuwar Hausa za mu yi amfani da su. Saboda haka, mun nemi su karanta sosai, domin ba za mu yi amfani da kalmomin da suka saba da su ba. Don haka, sun yi matukar kokarin ba mu abin da muke so. Alhamdulillahi aiki ya tafi daidai wa daida.

film/sarki_jatau/hausa_leadership_article.txt · Last modified: 2015/07/22 03:15 (external edit)