User Tools

Site Tools


producer:2_effects_empire.

2 Effects Empire

2 Effects Empire, sananniyar kungiya ce da take shirya fina finan hausa a Arewacin Tarayyar Nigeria.

2 Effects Empire, kungiya ce da tafi kowace kungiyar shirya fina finan hausa samun nasara a fagen shirya fina finai. Domin kuwa kungiyar ta samu nasarorin fina finai da dama a cikin kasar Nigeria dama kasashen waje.

Sani Musa Danja, Director ne Producer ne Mawaki ne Makidi ne kuma Shahararren Actor ne a fagen shirya fina finan hausa.

Yakubu Muhammad, Director ne Producer ne Mawaki ne kuma Makidi ne, sannan Marubucin Jarida ne.

Wadannan mutane guda biyu sune shugabannin wannan kungiya, kuma akwai 'yayan wannan kungiya da dama Maza da Mata. Kadan daga cikinsu sun hada da Ubale Ibrahim, TY Sha'aban Shaba, Bashir Qaya da Samira Ahmad.

Don haka wannan shafi zai kunshi labarai da rahotonni, tallan sababbin fina finan wannan kungiyar da sharhinsu. Tarihin 'yayan kungiyar da sauran abubuwa masu muhimmanci duk game da 2 Effects Empire. (Retrieved from http://twoeffectsempire.blogspot.com/2010/04/2-effects-empire.html)

A karshe, Allah (S.W.A) ya daukaka wannan kungiya ta 'yayanta baki daya.

Mutanen Kungiyar

Filmography

Films

Share this page

producer/2_effects_empire.txt · Last modified: 2015/08/12 22:56 by admin