Assalamu'alaikum. A Yanzu Haka kuma muna Tare da @alinuhu. #TareDaAliNuhu
Kowa ya bude kunnen Shi.
— Hausa Proverbs (@Bahaushee) September 12, 2015
@alinuhu. ka jima kana yin harkar Fim, wane irin cigaba harkar Fim ta samu Daga lokacin zuwa Yanzu? @alinuhu
#TareDaAliNuhu
— Hausa Proverbs (@Bahaushee) September 12, 2015
Ingantattun labarai, yanayin kayan aiki da makamantansu duk sun sauya. https://t.co/EVyaUfEcxA
— ali nuhu (@alinuhu) September 12, 2015
@alinuhu kana daya Daga cikin manyan Jarumai Na Kannywood, kuma ka samu lambobin girma da yawa, shin mi nene sirrin?
#TareDaAliNuhu
— Hausa Proverbs (@Bahaushee) September 12, 2015
Juriya, jajircewa da mai da hankali kan aiki. https://t.co/DXHUpbMqyd
— ali nuhu (@alinuhu) September 12, 2015
Ranka ya dade, @alinuhu. Ko wane irin dabaru ne suke dauke da kai har tsawon wannan lokaci, ana ci gaba da damawa da kai? #TareDaAliNuhu
— IG: HausaTrends (@HausaTrends) September 12, 2015
Wannan kuma yin Allah ne saboda a Fagge irin wannan mutum bashi da dabara. https://t.co/f3uvFi5Haw
— ali nuhu (@alinuhu) September 12, 2015
@alinuhu. shin ko kaine jarumi Na Farko Daga Kannywood daya shiga Nollywood? Mi yaja hankalin Ali Nuhu?
#TareDaAliNuhu
— Hausa Proverbs (@Bahaushee) September 12, 2015
Akwai irinsu Ibrahim Mandawari da Sani Muazu da Magaji Mijinyawa da Kasimu Yero duk sun rigani. https://t.co/L91T6oOSnC
— ali nuhu (@alinuhu) September 12, 2015
Tsakanin Nollywood da Kannywood, shin wa nene Ali Nuhu yafi Jin dadin fitowa a cikin fina-finan su? @alinuhu
#TareDaAliNuhu
— Hausa Proverbs (@Bahaushee) September 12, 2015
Kannywood, don ba a raina mafari. https://t.co/eM9BcQVw4A
— ali nuhu (@alinuhu) September 12, 2015
@alinuhu kwanakin baya tunda Daga lokacin siyasa har bayan ta, wasu Na ganin kamar an samu rabuwar Kai tsakanin Yan Fim, Yaya abun yake?
— Hausa Proverbs (@Bahaushee) September 12, 2015
Babu rabuwar kai, muna nan tsintsiya madaurin ki daya. https://t.co/7Ho7bXYQnr
— ali nuhu (@alinuhu) September 12, 2015
@alinuhu Ko wanne yunkuri kuke yi a yanzu wajen ganin kun kubutar da kanku daga zarge-zargen cewa ba kwa raya al'adun Hausa? #TareDaAliNuhu
— IG: HausaTrends (@HausaTrends) September 12, 2015
@HausaTrends Amma a kullum nakan ce "Wanda ya raina tsayuwar wata ya has ya gyara"
#TaredaAliNuhu
— ali nuhu (@alinuhu) September 12, 2015
Mutane suna yawan tsokaci Akan yadda ake sanya tufafi da kuma Yanayin fina-finan Nollywood, mi zaka ce Akan wannan? @alinuhu #TareDaAliNuhu
— Hausa Proverbs (@Bahaushee) September 12, 2015
Yawanci fina finan kudu fa labarin kudu suka kunsa saboda dole suturinsu su nuna haka. https://t.co/WjFhkDB5sh
— ali nuhu (@alinuhu) September 12, 2015
Wasu Yan Fim kamar Na Hollywood da Nollywood suna shiga siyasa bayan wani lokaci, ko Ali Nuhu nada ra'ayin shiga nan gaba? @alinuhu
— Hausa Proverbs (@Bahaushee) September 12, 2015
Gaskiya bani da ra'ayin siyasa https://t.co/kZcqXDto8i
— ali nuhu (@alinuhu) September 12, 2015
@alinuhu Ba ka ganin alaka da Gwamnati zata taimaki HausaFim, yadda ta taimaki Hollywood, Bollywood...? Me zai hana ku gyarota da gwamnati?
— IG: HausaTrends (@HausaTrends) September 12, 2015
Gwamnatin yanzu ba lallai sai yan fim sun shiga siyasa ba.Tana duba dacewa da cancanta ne a duk al'amuranta. https://t.co/Hik39qYkwG
— ali nuhu (@alinuhu) September 12, 2015
Daga Karshe, shin ta Yaya zaku daukaka martabar Hausa a idon duniya musamman ta fannin raya al'adu da kuma yada su? @alinuhu #TareDaAliNuhu
— Hausa Proverbs (@Bahaushee) September 12, 2015
Ta hanya samun hadin yan kallo, ma'ana su rika siyan fina finan da jigon su ya shafi al'adu. https://t.co/dKKXDCXf6t
— ali nuhu (@alinuhu) September 12, 2015
@alinuhu A karshe za mu so mu ji irin burin da kake da shi a nan gaba a harkarka ta HausaFim...? #TareDaAliNuhu
— IG: HausaTrends (@HausaTrends) September 12, 2015
Buri na ya kan zama sirri har sai ya tabbata mutane sa gani. https://t.co/fnK9vObTHO
— ali nuhu (@alinuhu) September 12, 2015
Mun gode daka kasance Tare damu, da fatan nan gaba mu samu wata dama mu tattauna sosai. Mun gode Bissalam. @alinuhu #TareDaAliNuhu
— Hausa Proverbs (@Bahaushee) September 12, 2015
Inn shaa Allah, nima na gode https://t.co/0ILDOxi7hd
— ali nuhu (@alinuhu) September 12, 2015