User Tools

Site Tools


film:makaryaci.

Maƙaryaci

Director Ali Gumzak
Producer Yakubu M Kumo
Starring Hafsa Idris, Sadiq Sani Sadiq
Released 2017

LABARI ne a kan wani matashi mai suna Zubairu (Sadiq S. Sadiq) mai son rayuwar k'arya, da son gwaninta. A irin rayuwar tasa ta k'arya ya kan je jami’a ba don ya na daga cikin d'aliban makarantar ba, sai don halayyar sa ta k'arya. A can ya had'u da wata d'aliba, Yasmin (Hafsat Idris), ya nace ya na son ta. Ita kuma ta na wulak'anta shi, sai daga baya ta so shi.

Labarin ya k'are ne a lokacin da Yasmin ta shigo gidan su Zubairu kakan sa ya kore su, sai dai an ce za a yi masa ci gaba.

ABIN YABO

Hoto da sauti kam sun fita rad'au.

KURAKURAI

* Ya kamata a sama wa labarin sunan da duk wanda zai d'aga shi zai so, amma MAK'ARYACI da aka sanya suna ne da tun a nan za a gane inda labarin ya dosa ba sai an sha wahalar ganin abin da ke cikin sa ba, kuma sunan ya yi yarinta ta yadda ba lallai ne manyan mutane su kalla ba.

* Zubi da tsarin labarin dai ga shi nan a tsaye babu wani karsashi da zai sa mai kallo d'okin ganin me zai tarar a gaba, domin ya san inda za a k'are, duk da akwai gurare da yawa da ya kamata a samar da cliffhanger, misali lokacin da Yasmin ta jizga Zubairu a makaranta.

* Sinasinai da yawa yanayin da Zubairu ya gabatar da su su na nuna taka-haye ya yi wa labarin, har mai kallo zai gane ba asalin Zubairun ya ke kallo ba, misali lokacin da su ka je Plaza da Yasmin.

* Wace makaranta ce ake maimaita aji sau sha uku ba tare da an kori d'alibi ba kamar yadda Naburaska ya fad'a?

* Bai kamata Zubairu ya ambaci ya tashi a cikin garori ga kakan sa ba, domin shi ba d'an daba ko d'an shaye-shaye ba ne ballantana a yi amfani da kowace kalma a bakin sa.

* A wajen cin abincin d'alibai su na da k'irjin d'an kwikwiyo da jaki kamar yadda Naburaska ya buk'ata a kawo masa, a wace jami'a ce? Kuma ba a bayyana mana k'abilar da su ke ba sa~anin Hausa; idan kuwa Hausawa ne kuma Musulmi mun sani Musulunci ya haramta cin wad'annan dabbobi.

* Duk lokacin da Zubairu zai yi waya a cikin makaranta ba a ta~a nuno shi ya fito da wayar ba. Ko da babu, ya kamata ita ma ya aro kamar yadda ya ke aro sutura.

* Duk k'aryar Zubairu ya kamata a nuno mana babban sanadin da zai dinga kawo shi makaranta, ba wai haka kawai ba.

* Da mota d'aya ake kai Zubairu cikin makaranta, amma wata d'aliba ta na ambatar motoci da yawa.

* A k'arshe, ina ba wa marubucin labarin nan shawara da ya daina yi wa labari gaggawa. A tsaurara binciken yadda rayuwar asalin mak'aryatan ta ke.

MAI SHARHI: Nura Sada Nasimat KT

Maƙaryaci Trailer

Share this page

film/makaryaci.txt · Last modified: 2017/12/15 00:59 by admin