User Tools

Site Tools


news:aminiya.dailytrust.com.ng:yar-fim-sadiya-gyale-ta-amerce.

’Yar fim Sadiya Gyale ta amerce

A ranar Juma’ar da ta gabata ce fitacciyar jarumar fim din Hausa, Sadiya Muhammad wacce aka fi sani da Sadiya Gyale ta amerce wanda ya kawo karshen barinta masana’antar fim din dungurungum.

Auren da jarumar ta yi shi ya kawo karshen rade-radin da ake yi cewa akwai alakar soyayay tsakaninta da jarumi Abubakar Baballe Hayatu, duk da yake jaruman sun sha musanta batun soyayay a tsakaninsu inda suke cewa akwai kyakkyar fahimta da abokantaka a tsakaninsu. An dauki tsawon shekaru rabon da a ga fuskar jarumar a cikin fina-finan Hausa, inda masu kula da al’amuran yau da kullum ke ganin cewa hakan ya faru ne sakamakon yin aure da aminiyarta kuma abokiyar sana’arta, Zainab Raga ta yi. Hakan ya sa jarumar ta dakatar da yin fim don ta mayar da hankalinta wajen sama wa kanta mijin aure. Aminiya ta rawaito cewa an daura auren jarumar tare da angonta Abubakar Muhammad ne a safiyar ranar Juma’a, a unguwarsu da ke Wudilawa. Angonta ya biya Naira dubu 50 a matsayin sadaki.

Ana ganin cewa aurenta yana daya daga cikin aure-auren da kusan dukkanin masu ruwa da tsakai a sana’ar fim suka halarta. Daga cikin wadanda suka halarta akwai Shehu Hassan Kano da Kabiru Miakaba da Ali Nuhu da Bala Anas Babinlata da sauransu. Daga cikin fina-finan da ta yi sun hada da Gyale da Gidan Gado da Jaraba da Gudun Kaddara da Gwamnati da Gwanaye da Jamhuriyya da Kishiya Ko Yar Uwa da Tutar So da Ummi da Gidan Iko da Gara da sauransu.

news/aminiya.dailytrust.com.ng/yar-fim-sadiya-gyale-ta-amerce.txt · Last modified: 2016/04/11 14:12 by admin